<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ƴan yaƙin Almasihu, ku sa sulkenku fa,
 Ku ɗauki kayan yaƙinsa, ku kafa dagarku.

[V2]
 2) Cike da Ruhunsa, da ƙarfi za ku tsaya
 Idan kun dubi Almasihu, za ku ci gaba dai.

[V3]
 3) Ku zare takobi, Maganar Allah ce.
 Kuma ku ɗauki garkuwarku, wato bangaskiya ce.

[V4]
 4) Karƙashin tutarsa kada ku ji tsoro.
 Ku fāda wa maƙiyanku, Shaiɗan da zunubi.

[V5]
 5) Da haka za ku tsaya, kome kashedinsu.
 Magauta za su ba ku baya, kome dai ikonsu.</lyrics>
<title>Ƴan Yaƙin Almasihu, Ku Sa Sulkenku Fa LW280</title>
<hymn_number>280</hymn_number>
</song>